Yaki da 'yan fashi teku a mashigin Guinea

Yaki da 'yan fashi teku a mashigin Guinea
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kuduri na karfafa yaki da ‘yan fashin teku a mashigin tekun Guinea, wanda ke zaman tunga ta masu ruwa da tsaki wajen fashin tekun.

Daftarin kudirin dokar da kwamitin sulhu ya amince da shi  ya bukaci mambobin kasashen yankin da su hukunta masu fashi da makami a cikin teku bisa tsarin dokokin kasa. Yankin ya sami rahotannin hare-hare 52 na 'yan fashi a cikin shekara ta  2021 adadin da ya yi kasa saboda matakan da ake dauka  idan aka kwatanta da na shekara ta 2020 inda aka samu hare-hare 115.

 

 


News Source:   DW (dw.com)