Rahotanni daga Beljiyam na cewa an soke tashin jiragen sama da dama a biranen Brussels da Charleroi, da kuma soke zirga zirgar kashi biyu cikin kashi uku na jiragen kasa sakamakon yajin aikin gama-gari kan batun fansho da manyan kungiyoyin kwadagon kasar suka tsunduma.
Wasu majiyoyi sun ce an soke kashi 40 cikin 100 na tashin jirage a filin jirgin saman Brussels da ke zama mafi girma a kasar, haka zalika kamfanin Ryanair mai amfani da filin jirgin saman Charleroi ya sanar da soke tashin illahirin jiragensa daga karfe 12 na wannan litinin din saboda rashin ma'aikata.
Gamayyar manyan kunkiyoyin kwadago uku na Beljiyam sun kira wannan gagarumin yajin aiki da ya raunana harkokin zirga-zirga ne domin yin kashedi ga gwamnatin hadaka ta kasar kan wani kudurin dokar fansho da ta gabatar wa majalisar dokoki.