Fafaroma Francis ya nuna goyon baya ga bukatar kaddamar da bicike kan zargin da ake yi wa Isra'ila na kisan kare dangi a zirin Gaza a cikin wani littafinsa da ya ke sa ran wallafawa kamar yadda jaridar Italiya ta La stampa ta ruwaito.
A cewar wasu daga cikin kalmomin da littafin ya kunsa abinda ke faruwa a Gaza ya na da alamun kisan kare dangi, dan haka akwai bukatar duba shi da tsanaki domin ganin ko ya yi dai-dai da abinda alkalan wasu kotunan duniya suka fada.
Paparoma ya nemi afuwar yaran da aka ci zarafinsu a coci
Isra'ila na sha suka a duniya saboda yawan fararen hula da yakin da take yi a Gaza ya shafa da kuma karancin kayan agaji.
Kasar Afirka ta Kudu ce ta gurfanar da Isra'ila a gaban kotun kasa da kasa da ke birnin Hague bisa zargin kisan kare dangi.
Fafaroma ya yi tir da kisan faren hula a Gabashin Kwango
Babban mai shari'a a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ya nemi a kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaron kasar Yoav Gallant da kuma shugabannin Hamas.