Kimanin mutane 10 aka tabbatar sun halaka zuwa yanzu sakamakon wutar dajin da ta tashi a Los Angeles da ke kasar Amurka. Sannan wutar da lalata kimanin gidaje dubu-10, yayin da masu kashe gobara ke aiki ba dare ba rana, domin shawo kan wutar.
Karin Bayani: Wutar daji ta kashe mutane bakwai a Amirka
An dai kwashe kimanin mutane dubu-180 daga gidajensu, yayin da aka yi gargadi ga kimanin mutane dubu-20 game da yuwuwar kwashe su muddun lamarin ya tsananta.
Tuni wutar ta lalata daji mai girman heta dubu-13. Mahukunta a Los Angeles da ke kasar ta Amurka suna fatan shawo kan wannan matsalar wutar dajin da take kara ta'azzara.