Mai shekaru 57 a duniya dan asalin kasar Habasha, ya yi tazarce a matsayin darakta janar na hukumar ta WHO din ne bayan da aka zabe shi da gagarumin rinjaye kasancewar ba shi da abokin hamayya. Tun dai a shekara ta 2017 ne, Tedros ya dare kan kujerara shugabancin hukumar ta WHO a matsayin dan asalin Afirka na farko da ya taba samun wannan mukami. A wancan lokaci ya yi alkawarin samar da harkokin kiwon lafiya cikin sauki ga kowa a baki dayan duniya, sai dai a shekara ta 2020 annobar corona ta sha kan al'amura baki daya. Tuni dai Tedros ya amince da sake zaben nasa da aka yi, cikin yanayi na zubar da hawaye.
An sake zabar shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus a matsayin shugaban hukumar a wa'adi na biyu.