WHO na bincike kan bullar Ebola a Kwango

WHO na bincike kan bullar Ebola a Kwango
An sake samun labarin bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, kasar da ke tska da rikicin hare-haren ta'addanci. Bai jima ba dai aka sanar da shawo kanta.

Hukumomin Lafiya a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, sun ce suna bin diddigi domin gano gaskiyar lamari a game da labarin sake kunno kai da aka ce cutar Ebola ta yi a kasar.

A farkon watan jiya ne dai Jamhuriyar Dimukuradiyyar ta Kwango mai fama da rashin zaman lafiya, ta sanar da kawo karshen cutar ta Ebola, watanni biyu bayan mutuwar wasu mutum biyar da ita a arewa maso yammacin kasar.

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce wannan shi ne karo na 14 da ake samun Ebola a Kwangon tun bayan bullar ta a Kwangon a shekara ta 1976.

Akwai dai fargabar cewa wata mata mai shekaru 46 da ta mutu a lardin Kivu da ke a gabashin kasar a aranar Litinin, ta harbu da kwayar cutar.


News Source:   DW (dw.com)