Cutar da ba a san asalinta ba ta barke har sau biyu cikin wannan shekarar a yammacin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce, an samu rahoton mutane 12 da suka fara rashin lafiya a yankin Bolamba yayin da wasu takwas suka rigamu gidan gaskiya a watan Janairun wannan shekarar. A farkon wannan watan na Fabarairu an samu rahoton mutane 158 da suka kamu da cutar, yayin da wasu 58 suka mutu a yankin Basankusu.
Karin bayani:Binciken cuta a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Alamomin cutar dai sun hada da zazzabi da ciwon kai da zufa da sankarewar wuya da ciwon gabobi da fitar da jini ta hanci da amai da kuma gudawa. Tuni dai aka tura da jami'an hukumomin dakile yaduwar cututtuka da kuma kwararru na WHO da su gudanar da bincike tare da gano kan cutar, musamman a cikin abinci da ruwan sha da kuma muhallansu. Sakamakon bincike farko-farko sun nuna dukanninsu ba su dauke da cutar Ebola ko Marburg, sai dai kuma yayin da ake kokarin gano asalin cutar, ana kokarin yi musu gwajin sankarau.