Jami'in na soja, ya mutu ne sakamkon tashin wata nakiya a lokacin da yake aikin sintiri a arewacin Mali.
Wani jami'i a rundunar MINUSMA wanda bai so a bayyana sunansa ba, ya ce jami'in da ya mutun, ya ji raunuka da aka kai shi asibitin birnin Kidal, kafin daga bisani rai ya yi halinsa a can.
Mutuwar jami'an sojan na Majalisar Dinkin Duniya, ta zo ne a lokacin da ake tattaunawa game da yiwuwar sabunta aikin rundunar a kasar.
Sojojin Majalisar Dinkin Duniyar 175 ne dai suka mutu a aikin sintiri da suke yi kawo yanzu.