Wani sabon nau'in cutar hanta ya bulla a Tuai

Wani sabon nau'in cutar hanta ya bulla a Tuai
Kwararru sun gano wata cutar hanta mai tsanani ta yara kanana da ba a san asalinta ba, wadda aka fara ganowa a Birtaniya da wasu kasashe guda hudu na Turai da kuma yammacin Amirka.

A cikin wata sanarwa da ta fitar cibiyar kula da cututtuka ta Turai (ECDC) ta ce an samu karin yara da ke dauke da kwayoyin cutar ta hanta a kasashen Denmark da Ireland da Holland da kuma Spain. Cibiyar ta ECDC ta ce cutar da ke kama yara 'yan shekara daya zuwa shida na somawa da amai da gudawa da ciwon ciki.

A halin da ake ciki masana da kwararru na ci gaba da gudanar da bincike a duk cikin kasashen da aka ba da rahoton bullar cutar aa Turai da Amirka domin gano asalinta.

 


News Source:   DW (dw.com)