Wani sabon nau'in cutar hanta ya bula a Tuai

Wani sabon nau'in cutar hanta ya bula a Tuai
Kwararru sun gano wata cutar hanta mai tsanani ta yara kanana da ba a san asilinta ba, wada aka fara ganowa a Birtaniya da wasu kasashe guda hudu na Turai da kuma yammacin Amirka.

A cikin wata sanarwa da ta fitar cibiyar kula da cututtuka ta Turai (ECDC) ta ce an samu karin yara da ke dauke da kwayoyin cutar a kasashen Denmark,da Ireland, da Holland da Spain. Cibiyar ta ECDC ta ce cutar da ke kama yaran 'yan shekara daya zuwa shida na somawa da amai da gudwa da ciwon ciki. A halin da ake ciki masana da kwararru na cigaba da gudanar da bincike a duk cikin kasashen da aka ba da rahoton bular cutar na Turai da Amirka domin gano asilinta.

 


News Source:   DW (dw.com)