Akalla mutum 26 ne aka tabbatar da cewa sun salwanta a wani hari da aka kai wa lardin Akwaya da ke a yankin kudu maso yammacin kasar Kamaru a karshen mako.
Rahotannin da ke fitowa daga yankin wanda ya yi kauren suna da miyagun ayyukan masu ikiraren ballewa daga Kamarun, na cewa harin na ranar Asabar ya ta'azzara lamura a tsakanin wadanda da ma ke fama da fitintinu na kabilanci da ma na ikon mallakar filaye.
Tun a shekara ta 2017 ne dai 'yan bindiga a yankin renon Ingila na Kamaru, suka kunna wutar rikici da gwamnatin Shugaba Paul Biya, saboda zargin maida su saniyar ware a kasar.
Sabon harin dai ya shafi mazauna kauyen Ballin ne, yankin kuma da ke iyaka da Najeriya.