Wanda ya kona Angulu zai yi shekaru 24 a yari

Wanda ya kona Angulu zai yi shekaru 24 a yari
Wani alkalin gundumar Monterey ya ce kotu ta yankewa Ivan Gomez mai shekaru 31 hukuncin ne don kashe Angulu ta hanyar cinnawa gandun daji wuta, yayin da yake noma tabar wiwi ba bisa ka'ida ba.

Masu gabatar da kara a Amirka sun ce an yanke hukuncin shekaru 24 a gidan yari kan mutumin da ya fara haddasa gobarar daji a shekarar 2020 a Carlifonia, wanda ya kashe angulu 12 tare da jikkata wasu manyan tsuntsaye da jefa rayuwar jami'an kashe gobara a cikin hadarin gaske.

A ranar 18 ga watan Agusta na shekarar 2020 ne gobarar ta tashi a gabar tekun tsakiyar arewa maso yammacin Los Angeles, inda ta lalata gidaje 10 da kadada 80 na gandun daji wanda tun a 1997 aka ware don 'yantar da angulu.


News Source:   DW (dw.com)