Von der Leyen za ta gabatar da sabuwar tawagar jami'an EU

Bayan shafe makonni ana jeka-ka-dawo a kan mutane da suka dace a yi aiki da su, ana sa ran daga bisani shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen za ta gabatar da sunayen sabbin jami'an hukumar a wa'adin mulkinta na biyu a ranar Talata.

Tawagar za ta fara aikin wa'adin shekara biyar a dai dai lokacin da duniya ke cikin kila-wa-kala sakamakon yake-yake.

EU ta fitar da makudan kudi domin tallafawa Ukraine

A bisa al'ada shugabar wacce ta fito daga Jamus za ta zabi mambobin tawagar tata ce daga cikin mutanen da kasashen EU 26 za su gabatar mata.

Tuni aka fara samun takaddama inda mutumin da Faransa ta gabatar Thierry Breton, ya ki amincewa da mukamin ministan kasuwancin cikin gida a ranar Litinin, ya kuma zargi Ursula von der Leyen da matsa wa Faransa lamba ta cire shi daga jerin sunayen sabbin jami'an.

Von der Leyen ta samu wa'adi na biyu na jagorancin EU

Ita ma von der Leyen burinta na tabbatar da daidaiton jinsi a tawagar tata bai cika ba saboda kasashe da dama sun gabatar mata da maza a matsayin wakilai maimakon mata.


News Source:   DW (dw.com)