A cikin sakon da ta wallafa a shafinta na twitter, shugabar hukumar kungiyar ta EU Ursula von der Leyen ta ce ta yi magana da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky, kuma tana fatan samun amsoshin tambayoyin zama mambobin Ukraine.
A watan Afrilu, von der Leyen ta ziyarci Kyiv don nuna goyon baya ga Ukraine kuma ta amince cewa Brussels za ta yi la'akari da dadewar burin Ukraine na shiga kungiyar.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da kasar Rasha ta yi bikin cika shekaru 77 kan nasarar yakin duniya na biyu a kan 'yan Nazi a kasar kasar Jamus. Amma kuma a jawabin da shugaban kasar Vladmir Putin ya yi, ya fi mayar da hankali ne a kan mamayar da kasarsa ke ci gaba da yi a Ukraine.