Volkswagen zai sayar da reshensa na China

Babban kamfanin kera motocin Jamus Volkswagen zai sayar da reshensa da ke lardin Xianjiang a China, yankin da Beijin ta yi kaurin suna wajen keta haddin bil Adama da suka hada da tilasta aikin karfi.

Wani mai magana da yawun kamfanin, ya ce kamfanin ya yanke hukuncin sayar da reshen nasa na China ne saboda daliliai na tattalin arziki.

Tun a shekarar 2023 kamfanin na Volkswagen ya fuskanci koma baya a China da ke zama babbar kasuwar da ya fi sayar da motocinsa.

Kamfanin motocin na Jamus ya sami koma baya wajen gogayya da kamfanonin cikin gida na China lamarin da ya sa ya rasa ciniki kamar yadda ya saba yi a baya.

 


News Source:   DW (dw.com)