A rahoton na UNICEF da ya fidda jajiberin bikin ranar yara Mata ta Duniya da za a yi, na nuni da cewar a duk cikin yara takwas akwai daya da ke fuskantar cin zarafi ko kuma ta taba fuskanta.
Kazalika rahoton ya kara da cewar adadin yaran mata da kananan yara a fadin duniya da suka taba zama wadanda wannan lamarin ya taba shafa sun haura mutane miliyan 650.
Lamarin ya tabarbare ne biyo bayan karuwar matsalar tsaro da ma annobar corona da aka yi fama da ita a baya.
Asusun na UNICEF ya ce yara maza ma na fuskantar wannan matsala ta cin zarafi ta hanyar fyade a yayin tasowarsu.