Mai magana da yawun Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijirar ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNHCR Eujin Byun ta shaidawa manema labarai cewa, yakin da ake fafatawa a birnin Goma na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ya tilasta kimanin mutane dubu 350 tserewa daga gidajensu tare da zama a filin Allah a yanzu haka.
A watan Janairun da ya gabata ne dai, kungiyar 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan makwabciyar kasa Ruwanda ta kwace iko da birnin Goma da ke zaman mafi girma a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon. Rahotanni sun nunar da cewa a yanzu haka kungiyar tawayen ta M23 na kutsa kai zuwa yankin kudancin Jamhuriyar Dimukuradiyyar ta Kwango, abin da mahukunta ke fargabar ka iya janyo tashin hankali na kan iyaka a yankin da dubban 'yan gudun hijira ke samun mafaka.