Ukraine: Zelenskyy ya yi tayin murabus idan kasar za ta shiga NATO

Ya ce idan za a sami zaman lafiyaa a Ukraine, Idan har lallai ana bukatar na sauka daga mukami na, a shirye na ke na sauka idan za a shigar da Ukraine cikin kungiyar NATO kamar yadda ya shaida wa yan jarida a wani taron manema labarai a Kiev babban birnin kasar.

Ya ce kara da cewa zai sauka nan take idan bukatar hakan ta zama wajibi.

Zelensky ya kuma kara da cewa yana son ganin shugaban Amurka Donald Trump ya zama abokin kawancen kasar Ukraine domin kara taimakawa amma ba kawai a matsayin mai shiga tsakanin Kyiv da Moscow ba.

Trump dai ya zafafa cacar baki da Kyiv inda ya zargi Ukraine da cewa ita ce ta janyo yakin sannan ya kira Zelensky a matsayin shugaban kama karya sakamakon soke zaben kasar saboda yaki.

Daga baya ya bukaci Putin da Zelensky su hada kai su kawo karshen yakin duk da mayar da Ukraine saniyar ware a tattaunawar baya bayan nan.

 


News Source:   DW (dw.com)