Von der Leyern ta ce, lokaci yayi da za a fara tunanin yadda za a gina Ukraine, a duk lokacin da aka kawo karshen yaki, inda ta kara da cewar EU na da sha'awar jagorantar aikin sake gina kasar.
A daya hannun kuma, EU za ta kashe makuddan kudi da yawansu zai kai Euro biliyan 300 nan da shekara ta 2030, kafin ta samu 'yancin cin gashin kanta daga dogaro da makamashin Rasha.
A halin da ake ciki dai, wani sojin Rasha da ake zargi da aikata laifukan yaki a Ukraine, a bangaren shari'ar farko da aka kaddamar tun bayan da Rasha ta mamaye kasar, ya amince da duk zarge zargen da aka yi masa.
Da aka tambayeshi a gaban kotu game da laifuffukan yakin da ke kansa, ciki har da kisan gilla, Sergeant Vadim Shishimarin mai shekaru 21 da haihuwa, ya amsa aikata laifukan.