Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin da kasar ke yi da Rasha aka fara kaiwa tashar hari, wanda ko a jiya ma'aikatan tashar suka sanar da fuskantar matsala bayan kama wuta da wasu na'urori suka yi.
Wannan tasha ta Zaporizhzia dai na fuskantar barazanar hari tun bayan da dakarun kasar Rasha suka sanar da karbe iko da yankin.
Yanzu haka hukumar da ke kula da makamashin nukiliya ta Duniya wato IAEA na shirin aika tawagar kwararu domin kai dauki ga tashar wadda ita ce mafi girma a nahiyar Turai.