Ukraine: Yunkurin ceto fararen hula a Azovstal

Ukraine: Yunkurin ceto fararen hula a Azovstal
Gwamnatin Ukraine ta yi kira da a gaggauta samar da wata kafa ta ficewa da fararen hular da suka makale a masana'antar harhada karafuna ta Azovstal da ke Mariopul bayan da Rasha ta karbe iko da garin.

A daidai lokacin da rundunar tsaron Rasha ta karbe iko da Mariopul, gwamnatin Ukraine ta yi kira da a gaggauta samar da hanyoyin ficewa da fararen hula da suka makale a masana'antar harhada karafuna ta Azovstal a Mariopul tare da sojan Ukraine da ke ci gaba da turjiya kan batun mika wuya.

Ministan harkokin wajen Ukraine ne ya bayyana haka a wannan Alhamis, sai dai ya bayyana cewa fararen hular da ke samun mafaka tare da sojan Ukraine ba sa son ficewa su bar dakarun Ukraine din da suka rage, kuma ba sa son dakarun Rasha su fita da su ba.

A sakonsa na Twitter ministan harkokin wajen Ukraine ya ce akwai bukatar a cikin gagga a hanzarta fitar da wata kafa da za fice da fararen hulan kana cikin yanayi na tabbatacen tsaro.


News Source:   DW (dw.com)