Shugaba Volodmyr Zelensky na Ukraine ya yi gargadin samun duniya na gab da shiga matsalar yunwa a saboda hana fitar da hatsi da ke jibge a tashoshin ruwan kasar da Rasha ke ci gaba da yi.
Da yake jawabi ga taron sulhu da ya gudana a Singapore ta kafar bidiyo, Zelensky ya ce abin da duniya ke fuskanta yanzu haka duk wasan yara ne, muddin aka ci gaba da tafiya a haka duniya za ta shiga wani hali na matsananciyar yunwa a kasashe da dama a nahiyar Afirka da Asiya da ba a ga irin ta ba.
Kazalika ya ce matsalar ta yunwa ka iya janyo rikice-rikicen siyasa da ka iya kai wa ga kifar da gwamnatoci.
Mahukuntan na Kiev na zargin Moscow da sace hatsin da suka hana a fitar da shi, a yayin da farashinn kayayyakin masarufi ke tashin gwauron zabi a kasuwannin duniya, Moscow na dora alhakin hakan an kan makwabciyarta Ukraine.