Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar Ukraine ya kori Andriy Melnyk jakadan kasar da ke Jamus daga bakin aiki, a wani kudirin doka da shugaban ya sanya hannu a kai. Sannan ya jakadun Ukraine a kasashe Norway, Jamhuriyar Czech, Hungari da Indiya duk an kore su daga bakin aiki.
Babu wani dalili da aka bayar kan matakin da shugaban kasar ya dauka, ko kuma makomar jakadun.
Shi dai Andriy Melnyk a matsayin jakadan Ukraine a Jamus ya yi fice wajen neman kayan yaki ga kasar domin mayar da martani bisa mamaya daga dakarun Rasha.