Shugaba Volodymyr Zelenskyy na kasar Ukraine ya yi zargin Shugaba Vladimir Putin da kokarin hada tashar ta Zaporizhzhya da wutar lantarki daga Rasha bayan katse wutar Ukraine.
Shugaba Zelenskyy ya ce wannan wani gagarumin shiri ne da Rasha ke yi domin fusata Ukraine.
Yanzu dai cibiyar na karkashin ikon Rasha ne, kuma kasashen biyu na ci gaba da aibanta juna kan hare-haren da ake kai wa cibiyar ta nukiliya mafi girma a nahiyar Turai.
A share guda kuwa, Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce za a bai wa jami'an Majalisar Dinkin Duniya damar ziyara tashar nukiliya ta Zaporizhzhya.
Fadar gwamnatin Rashar ta fadi hakan ne bayan wayar tarho da Shugaba Putin ya yi da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron.