Ukraine ta bukaci dakatar da Rasha a FAO

Ukraine ta bukaci dakatar da Rasha a FAO
Shugaban kasar Ukraine ya bukaci a dakatar da kasar Rasha a hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya saboda haddsa tashin farashin abinci a duniya.

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya bukaci ganin an kori kasar Rasha daga cikin hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, inda ya zargi mahukuntan Moscow da haddasa rikicin da duniya ke fuskanta sakamakon kutse a kasarsa. Ukraine ta zargi Rasha da kawo cikas wajen jigilar abinci a gaban tekun kasar saboda yakin da ke faruwa. Ita dai hukumar abinci ta duniya, FAO, tana aiki a kasashe kimanin 130 na duniya.

A wani labarin gwamnatin Ukraine ta ce sojojin kimanin 100 suke kwanta dama kowace rana sakamakon yakin da ke faruwa bayan Rasha ta kaddamar da kutse. Sannan akwai daruruwan sojoji da suka samu raunika a fagen yaki.

Sojojin na Ukraine suka ci gaba da fafatawa mai zafi a wasu yankuna na gabashin kasar da dakarun Rasha ci gaba da dannawa.

 


News Source:   DW (dw.com)