Shugaba Vladimir Putin ya bayyana hakan ne ga shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz cikin wata tattaunawa da suka yi ta wayar tarho. Ya nunar da cewa a shirye Rasha take ta samar da hanya mai sauki ta fitar da hatsin, yana mai cewa kara yawan fitar kayan amfanin gona da kuma takin zamani daga Rasha zai taimaka gaya. Sai dai Putin ya ce, tilas sai an cire takunkumin da ke da alaka da sayen kayan amfanin gona daga Rashan da aka kakaba mata bayan da ta mamaye Ukraine.