Ukraine: Rasha ta tsagaita wuta a Mariupol

Ukraine: Rasha ta tsagaita wuta a Mariupol
Sanarwar Rashan ta wannan Litinin ta ce ta yi haka ne domin bayar da dama a kwashe fararen hular da ke zaune kusa da kamfanin a wannan gari mai teku da Ukraine da Rasha suka kwashe makonni suna ''tata-burza' da makamai.

Dakarun Rasha sun sanar da tsagaita wuta a kusa da wani kamfanin sarrafa karafa na birnin Mariupol a Ukraine. Sai dai kuma, a wasu yankuna na Ukraine, ana zargin Rasha ta kaddamar da hare-hare kan tashoshin jiragen kasa.

Wannan na zuwa ne a yayin da ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta musanta yunkuri na gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a domin karbe iko da yankin Kherson na kudancin Ukraine. A ranar Jumma'ar da ta gabata ce dai Shugaba Volodymyr Zelenskyyna Ukraine ya zargi mahukuntan Moscow da wannan kokari.


News Source:   DW (dw.com)