Ukraine: Rasha ta bude tashar jiragen ruwa

Ukraine: Rasha ta bude tashar jiragen ruwa
Rasha ta sanar da sake bude tashar jiragen ruwa ta kudancin Ukraine da ke birnin Mariupol, bayan da sojojin Moscow suka karbe iko da birnin da ke kusa da Tekun Azov.

Kakakin ma'aikatar tsaron Rashan Igor Konashenkov ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai, inda ya ce tuni gabar ruwan ta koma bakin aiki yadda ya kamata.  Birnin da ke da matukar muhimmanci, ya fada hannun dakarun Rasha bayan da ta fara mamaya a Ukraine din. Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci mahukuntan na Rasha da su kyale a wuce da tarin abincin da ke tashoshin jiragen ruwan Ukraine, domin kaucewa fadawa cikin matsanancin halin yunwa a duniya. Mataimakin ministan harkokin kasashen ketare na Rashan Andrei Rudenko ya ce kasarsa na aiki ne kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bukata, yana mai cewa a shirye suke su shirya tare da raka kayan abinci zuwa inda ya kamata in har mahukuntan Ukraine sun cire nakiyoyin da suka dasa a kewayen tashoshin jiragen ruwan.

     

 


News Source:   DW (dw.com)