Ukraine da Moldova na hanyar shiga Tarayyar Turai

Ukraine da Moldova na hanyar shiga Tarayyar Turai
Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana shirin fara bin matakan karbar kasashe Ukraine da Moldova inda suka kasance 'yan takara na shiga kungiyar.

Hukumar Tarayyar Turai ta amince da matakin kasashen Ukraine da Moldova na zaman 'yan takara kan shiga kungiyar. Yayin taron manema labarai a birnin Brussels na kasar Beljiyam helkwatar kungiyar, shugabar hukumar Ursula von der Leyen ta ce kasar ta Ukraine ta zama 'yar takara kan shiga kungiyar duk da yake akwai sauran aiki. Kana ta ce kasar Moldova za ta kara zage damtse kan bunkasa tattalin arziki da karfafa tafiyar da gwamnati.

Shugaba Volodymyr Zelensky na Uktaine ya wallafa sako a kafar sada zumunta da ya nuna gamsuwa da matakin na kungiyar kasashen Tarayyar Turan. Tuni Shugaba Maia Sandu ta kasar Moldova ta yi maraba da wannan mataki kan kama hanyar shiga kungiyar ta Tarayyar Turai mai tasiri.

 


News Source:   DW (dw.com)