Turmutsitsi ya yi ajalin masu karbar kyautar abinci a Abuja

Mutane masu yawa sun rasa rayukansu a yayin wani turmutsitsi da ya faru a wajen rabon kyautar kayan abincin Kirsimeti a wata coci da ke Abuja, fadar gwamnatin Najeriya.

Tuni dai shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya soke halartar wasu bukukuwan karshen shekara da ya so halarta a wannan Asabar domin nuna alhini da girmama rayukan mutanen da suka mutu a turmutsitsin na neman kyautar abincin. Shugaban na Najeriya ya ce duk da cewa wannanlokacina murna da nuna kaunar juna ne, amma  rasa rayuka da aka yi ya girgiza shi matuka, yana mai fatan samun salama ga wadanda suka rasa rayukan nasu.


News Source:   DW (dw.com)