Turkiyya za ta sulhunta Ruwanda da Kwango

A ganawarsa da Shugaban Ruwanda Paul Kagame, Shugaba Recep Tayyib Erdogan ya ce gwamnatin Ankara a shirye take domin bayar da goyon bayanta wajen sasanta rikicin da ke barazana ga zaman lafiyan yankin. Hakan dai na zuwa ne yayin da Turkiyya ke kokarin kara yaukaka dangantakar diflomasiyya da kuma tattalin arziki da kasashen Afirka. 

Karin bayani: Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango za ta yi sulhu da Ruwanda

Alkalumman Majalisar Dinkin Duniya sun yi nuni da cewa, fiye da mutane 400,0000 ne a wannan shekarar suka rasa matsugannansu sakamakon rikice-rikice a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango. Kakakin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR Matthew Saltmatsh ya ce, adadin mutanen sun nunka alkalumman da aka sanar a makon da ya gabata.

Mayakan M23 na Ruwanda na ci gaba da gwabzawa da dakarun Kwango inda suka kara kaimi wajen kewaye birnin Goma na arewacin yankin Kivu. 

    


News Source:   DW (dw.com)