Turkiyya za ta dauki matakin soji a Siriya

Turkiyya za ta dauki matakin soji a Siriya
Turkiyya na shirin daukar matakin soji a kan mayakan kurdawa na YPG da ke arewacin Siriya. Ankara na ganin rashin mutunta yarjejeniyar da aka cimma na yin nesa da iyakarta na barazana ga tsaron kasar.

Shugaba Racep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya bayyana shirinsa na yin amfani da karfin soji a yankin arewacin kasar Siriya a yayin da Rasha wacce ke goyon bayan Siriyar ke ci gaba da luguden wuta a Ukraine.

Ankara ta sha alwashin kaddamar da hari a kan mayakan kurdawa na YPG da ke iyakar kasashen biyu.  A wata tattaunawa da Erdogan ya yi da Shugaba Vladmir Putin na Rasha ta wayar tarho, ya bayyana masa cewa yarjejeniyar da suka cimma a shekarar 2019 ta ajiye tazarar a kalla kilomita 30 har yanzu ba ta fara aiki ba. wanda ya ce hakan na barazana ga tsaron kasar.

kasashen Rasha da na Siriya gami da Amirka na da dakarunsu a wannan yanki da ke da iyaka da Turkiyya, sai dai Turkiyya har gobe ta na yi wa mayakan na Kurdawa kallon 'yan ta'adda da ke da alaka da jam'iyya PKK.


News Source:   DW (dw.com)