Wata kotu a birnin Santanbul na Turkiyya ta yanke wa attajirin nan Osman Kavala hukuncin daurin rai-da-rai. Sai dai a ranar Juma'ar da ta gabata, Kavala, ya musanta zarge-zargen. Tun a shekara ta 2013, hukumomin Turkiyya ke tsare da attajirin mai shekaru 64 a kan wadannan zarge-zargen da kotu ta ce ta tabbatar da su a wannan Litinin.
Hukuncin ya biyo bayan samun sa da lafin shiga wata zanga-zanga a 2013 da kuma samun sa da kotun ta ce ta yi da hannu wurin kitsa wa Shugaba Recep Tayyip Erdogan juyin mulkin da bai yi nasara ba a shekara ta 2016.