Turkiyya ta rufe kafofin isar da labaran Deutsche Welle ta Intanet daga yada shirye-shirye a kasar, matakin kuma da ya shafi harsuna 32 da tashar ke watsa shirye-shiryenta.
Haka ma baya ga tashar Deutsche Welle da Turkiyyar ta toshe, matakin ya kuma shafi tashar muryar Amirka wato VOA.
Cikin watan Fabrairun da ya gabata ne dai hukumar kula da harkokin watsa labara a Turkiyya, ta bukaci kafofin watsa labarai na duniya ciki har da Deutsche Welle da su nemi lasisin kasar kafin su watsa shirye-shirye a kasar.
Tashar DW dai ba ta nemi lasisin ba, saboda yin hakan zai sanya kasar bisa matsayi na tace shirye-shiryen da za ta watsa a kasar.
Cikin wata sanarwa, babban darakta tashar Deutsche Welle, Peter Limbourg ya ce an tattauna baki da baki da ma a rubuce da hukumomin na Turkiyya a kan dalinan da suka sa tashar ba za bukaci lasisi daga Turkiyya ba.
Tuni dai wannan batu yake ta wadari a shafukan sada zumunta a Turkiyya tun a ranar Alhamis da matakin ya fara aiki.