Turkiyya ta kaddamar da wata cibiya da ta ware domin tarbar kayan abincin da aka yo fitonsa daga Ukraine a karkashin yarjejeniyar fitar da hatsin Ukraine, a karon farko tun bayan da Rasha ta yi wa Ukrane kutse.
Ministan tsaron Turkiyya Hulusi Akar ne ya kaddamar da cibiyar da za a rika sauke kayan abincin da aka fito da su ta tekun Bahr Aswad daga tashoshin jiragen ruwa guda uku na kasar Ukraine
Hakan ta tuni ta sanya farashin alkama ya fara sauka a kasuwannin duniya. To sai dai harin makamai masu linzamin da Rasha ta kai wa tashar jirgin ruwa ta Odesa, daya daga cikin inda ake fitar da kayan abincin na Ukraine, ya haifar da shakku kan yiwuwar dorewar wannan yarjejeniya.