Turkiyya na son habaka arzikin Falasdinu

Turkiyya na son habaka arzikin Falasdinu
Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya sanar da wasu jerin yarjejeniyoyin da aka cimma a birnin Ramallah domin tallafa wa tattalin arzikin yankin Falasdinu da ke cikin hali na tsaka mai wuya

Wannan ziyarar dai ita ce ta farko da wani babban jami'an Turkiyya ya kai yammacin gabar kogin Jordan, wadda ta bayar da damar kulla yarjejeniyoyi  a fannonin noma da ilimi da kasuwanci da Falasdinu. Dama a farkon wannan wata, bankin duniya ya yi kira ga kasashen duniya da su kara yawan taimakon da suke bai wa gwamnatin Falasdinu sakamakon matsalar kudi da ta ke fuskanta.

 Turkiyya dai ta dade tana goyon bayan al'ummar Falasdinu, amma ziyarar da take kaiwa a yankin yammacin kogin Jordan ta ragu bayan rikicin diflomasiyya na tsawon shekaru 15 tsakanin Ankara da Isra'ila.

Ana sa ran gobe Laraba Mr. Cavusoglu zai gana da jami'an Isra'ila, a wani mataki na ziyarar farfado da huldar diflomasiyya tsakanin Ankara da kasar ta Isra'ila. 


News Source:   DW (dw.com)