Turai za ta sake fuskantar katsewar gas

Turai za ta sake fuskantar katsewar gas
Rasha za ta dakatar da tura mkamashin Gas dinta zuwa nahiyar Turai daga bututun Nord Stream 1, sakamakon wasu muhimman ayyuka na kwanaki da ta ce za ta gudanar a karshen wannan wata na Agusta.

A cikin wata sanarwar da ya fitar kamfanin Gazprom ya ce aikin gyaran bututun zai shafe tsawon kwanaki uku, kana za a samu raguwar makamashi kamar yadda aka saba da kasa da Cub-miter miliyan 33 a rana, lamarin da zai kara haddasa karancinsa a Turai a daidai lokacin da ake tsaka da bukatar makamashi. Sabon matakin na gwamnatin Rasha ya kara zafafa muhawarar da ta karade nahiyar Turai na zargin ko Rasha na amfani ne da makamashi a matsayin makamin yaki, tun bayan da ta shiga takun saka da manyan kasashen Yamma da suka nuna adawa da mamayar da take yi wa Ukraine. Duk da takun sakar da ke tsakaninta da Turai, Rasha na samarwa nahiyar kaso 40 cikin 100 na makamashin gas, sai dai a baya-bayan nan yana fuskantar katsewa daga Rasha saboda abin da ta bayyana da gudanar da muhimman aikace-aikace a bututan Nord Stream 1 da ke dakonsa zuwa Turan.

 


News Source:   DW (dw.com)