Hukumar kungiyar Tarayyar Turai ta gabatar da shirin cire kudin fito kan duk kayayyakin da ake shigowa da su kasashen kungiyar daga kasar Ukraine, domin taimakon kasar ci gaba da bunkasa tattalin arziki sakamakon kutsen Rasha.
Kwamishinan kula da tattalin arziki na kungiyar Valdis Dombrovskis ya ce matakin zai taimaki Ukraine karfafa fitar da kayayyaki zuwa kasashen Turai. Muddun 'yan majalisar dokokin kungiyar kasashen Tarayyar Turai suka amince da matakin, haka zai saka Ukraine shiga da kayayyaki zuwa kasashe 27 na tarayyar Turai ba tare da kudin fito ba.
Tun farko babban jami'ar hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen ta ce tana tattaunawa da Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar ta Ukraine kan hanyar taimakon tattalin arzikin kasar da ke cikin mawuyacin hali, inda Asusu ba da lamuni na duniya, IMF ke cewa tattalin arzikin kasar ta Ukraine zai gamu da koma baya sakamakon kutsen Rasha.