Kotun ta sanar a Alhamis din nan cewa tsohon ministan zai iya ci gaba da kudurinsa na tsayawa takara, tana mai bukatar a mayar da sunansa cikin jerin'yan takara.
Hukumar zaben kasar ce dai ta fara tsame sunan Zenaidi daga jerin 'yan takara bisa wasu zarge-zarge da kotu ta ce ba ta amince da su ba. Dan takarar ya kasance gaba-gaba cikin mutanen da suka yi kaurin suna wajen sukar shugaba mai ci Kais Saied wanda ke neman tazarce a zaben da ke tafe.
Masu sanya ido kan siyasar Tunisiya na cewa sake dawo da sunan tsohon ministan, ka iya zama karfen kafa ga Shugaba Saied, inda ake sa ran dan siyasar ya yi gogayya da shugaban da ake zargi da zama dan kama karya tun bayan da ya rusa majalisar dokoki ya yi wasu sauye-sauye a kasar da ke zama kariya ga kujerarsa ta shugaban kasa.