Marigayi Horst Koehler wanda ya shugabanci Jamus a daga shekarar 2004 zuwa 2010 shi ne shugaban kasa na farko da aka yi a kasar da bai da wata alaka da siyasa.
Karin Bayani: Shekaru 80 da 'yantar da sansanin Auschwitz
Marigayi Horst Koehler tsohon shugaban kasar Jamus da matarsa Eva KöhlerHoto: Ben Kriemann/PIC ONE/dpa/picture allianceA karshen shekarar 2009 aka sake zaben sa a matsayin shugaban kasa, amma ya yi ritaya bayan wata tataunawa da ya yi da ta janyo cece-kuce a fadin kasar. Marigayin ya rasu ya bar mai dakinsa Eva Kohler tsohuwar malamar makaranta da 'ya'yansa biyu da jikoki hudu.
Tsohon jakadan Majalisar Dinkin Duniya kuma masanin tattalin arziki ya shugabanci Asusun ba da lamuni na duniya, IMF a birnin Washington na Amurka.