A cikin wani sakon murya da aika wa magoya bayansa na jami'iyyar APRC, Jammeh ya ce yana shirin sake jagorantar jam'iyyarsa kuma ba zai sake amincewa da kowa ba. Shugaban ya kara da cewa, wadanda suke yi masa barazanar aikasa zuwa gidan yari su jiran dawowarsa. Kalaman Jammeh na zuwa ne wata guda bayan da kungiyar ECOWAS ta goyi bayan kafa wata kotun hadaka ta musamman da za ta hukunta laifukan da aka aikata a lokacin mulkinsa.
Gwamnatin Gambiya a shekarar 2022 ta amince da shawarwarin kwamitin da ya yi nazari kan ta'asar da aka yi a karkashin mulkin Jammeh, inda hukumomin kasar suka amince da gurfanar da mutane 70 ciki har da tsohon shugaban kasar.
Shugaba Jammeh ya jagoranci Gambiya da ke yammacin Afirka na tsawon gomman shekaru, an zargi gwamnatinsa da azabtar da mutane, da kisa da kuma cin zarafi bil Adama. Shugaban da ke samun mafakar siyasaa Equatorial Guinea tun a shekarar 2017, bayan ya fadi zaben da ya bai wa shugaba mai ci, Adama Barrow nasara har yanzu yana da dimbin masoya a Gambiya.