Tsohon firaministan Guinea Ibrahima Fofana zai sha dauri

Kotu ta musamman a Guinea ta yanke wa tsohon firaministan kasar Ibrahima Kassory Fofana hukuncin daurin shekaru 5, tare da cinsa tarar francs biliyan 2 na kasar, kwatankwacin dalar Amurka $230,000, bayan samunsa da laifin almubazzaranci da dukiyar kasa karkashin mulkin tsohon shugaban kasar Alpha Condé.

Kotun da ke Conakry babban birnin kasar, ta same shi da almudahnanar dala miliyan da dubu dari bakwai, daidai da francs biliyan 15 na kasar, wadanda aka ware domin aikin rigakafin cutar Corona da sauran kayan agajin jin kan al'umma.

Karin bayani:An ji karar harbe-harbe a fadar shugaban Guinea Conakry

Mr Fofana ya rike mukamin firaminista daga watan Mayun shekarar 2018 zuwa Satumban 2021, inda sojoji suka kama shi a cikin watan Afirilun 2022 bayan juyin mulkin da suka yi, ko da yake lauyoyinsa sun musanta zargin aikata laifin, inda suka ce bita-da-kullin siyasa kawai ake masa.

Karin bayani:Sojojin Guinea sun rusa jam'iyyu da dama a kasar

Guinea Conakry da ke hannun Kanal Mamadi Doumbouya, na daga cikin kasashen Afirka da ke karkashin ikon sojoji da suka hada da Mali, Jamhuriyar Nijar da kuma Burkina Faso.


News Source:   DW (dw.com)