Tsofaffin shugabannin Amurka za su halarci jana'izar Carter

Shugaba Joe Biden zai gabatar da jawabi a harabar cocin Episcopal da ke kasancewa wajen da ake gabatar da jawabai kan kyawawan halayyar tsofaffin shugabanni wanda ke zama al'ada tun daga lokacin Dwight Eisenhower da Ronald Reagan har zuwa zamanin  George H.W. Bush.

karin bayani: Tshohon shugaban Amurka Jimmy Carter ya mutu yana da shekaru 100: 

Tsofaffin shugabannin kasar Bill Clinton da George W. Bush da Barack Obama har ma da shugaba mai jiran rantsuwa Donald Trump zasu halarci jana'izar tare wasu mutanen sama da 3,000. Za dai a binne Carter a kusa da kabarin matarsa Rosalynn Carter a mahaifarsa da ke Georgia.

 


News Source:   DW (dw.com)