Tsigaggen shugaban Koriya ta Kudu ya gagara kamuwa

Masu bincike a Koriya ta Kudu sun fice daga gidan tsigaggen shugaban kasar Yoon Suk Yeol bayan shafe kusan sa'o'i shida ba tare da nasarar kama shugaban ba.

Wannan shi ne sabon rikicin siyasa da kasar ta gani a baya-bayan nan wanda ya kassarata bayan tsige shugabanninta biyu a cikin wata guda.

Tshon shugaban Koriya ta Kudu na bijire wa yunkurin kama shi

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar ta janye masu bincikenta bayan jami'an tsaro dake gadin Mista Yeol sun haramta musu kutsawa cikin gidansa sakamakon tsaron lafiyarsu.

Hukumar ta yi Allah wadai da halin da tsohon shugaban ya nuna na kin amincewa da bin doka bayan zarge-zarge da ake masa.

Koriya ta Kudu ta tsige sabon shugaban kasar

An shafe makonni ana kokarin mista Yeol ya bayyana don amsa tambayoyi amma ya rika sulalewa masu bincike kuma ganin baya-baya da aka yi masa shi ne na ranar 12 ga Disambar 2024.


News Source:   DW (dw.com)