Tsaurara matakan yakar cin-hanci a Vietnam

Sai dai masu fashin baki na yi wa kiran na shugaban Vietman din To Lam kallon wani mataki da ake amfani da shi, domin cimma buri a rikicin cikin gida da jam'iyyar ke fama da shi. Lam da ya yi jawabinsa na farko ga majalisar dokokin ta Vietnam ya karbi jagorancin jam'iyyar ta Communist ne a watan Agustan bana, bayan rasuwar tsohon jagoranta Nguyen Phu Trong da ya assasa yaki da cin-hancin na ba sani ba sabo. Yaki da cin-hancin a Vietnam dai, ya rutsa da mutane da dama da suka hadar da manyan 'yan kasuwa da jami'an gwamnati ciki har da shugabannin kasa biyu da kuma mataimakan firaminista uku daga shekara ta 2021 kawo yanzu. Shugaba Lam ya dora daga inda wanda ya gada ya tsaya, duk da ana zargin suna yakin ne domin cin dunduniyar 'yan adawa. Koda a makon da ya gabata ma dai, kafar yada labaran Vietnam din ta ruwaito alkalin alkalan kasar Le Minh Tri na bayyana cewa a shekarar da ta gabata an gurfanar da sama da mutane dubu 10 cikin shari'u kimanin 4,800 da Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa ta gudanar.


News Source:   DW (dw.com)