Tsananin zafi ya kashe mutane a Indiya

Tsananin zafi ya kashe mutane a Indiya
Akalla mutane 25 sun mutu a jihar Maharashtra da ke yammacin Indiya sakamakon tsananin zafi, hukumomi sun ce wannan shi ne adadin mutuwa mafi yawa cikin shekaru biyar da suka gabata.

Kasar Indiya ita ce kasa ta biyu a duniya wajen samar da alkama, amma yanayin zafi na shirin durkushe harkokin noma a bana sakamakon karancin ruwan sama da ake fuskanta sakamakon sauyin yanayni da kasar ke fuskanta tsawon shekaru biyar a jere. A watan Maris na shekarar 2022, kasar Indiya ta fara fuskantar tsananin zafi daga maki 33.1 a ma'aunin celsius zuwa sama da maki 40 a wasu yankunan kasar. Yanzu haka dai masana na gargadin cewa akwai yuwar zafin zai shafi lafiyar mutane da dama a yankunan da suke fuskantar tsanani zafi a kasar.


News Source:   DW (dw.com)