Wasu hare-hare biyu na kwanton bauna sun kai ga mutuwar sojojin bakwai na kasar Burkina Faso gami da wasu dakaru hudu wadanda suka kai dauki. An kai hare-hare a yankin arewacin kasar mai fama da tashe-tashen hankula.
Rundunar sojan kasar ta ce 'yan ta'adda suka kai hare-hare, kuma akwai wasu mutane tara da suka jikata.
Sabuwar gwamnatin mulkin sojan kasar ta Burkina Faso ta bayyana tsaro kan abin da za ta mayar da hankali, inda sojoji suka kifar da gwamnatin farar hula da suke gani ta gaza wajen magance yanayin rashin tsaro da kasar ta samu kanta a ciki.