Tsagaita bude wuta a Yemen

Tsagaita bude wuta a Yemen
Majalisar Dinkin Duniya ta ba da sanarwar tsawaita wa'adin tsagaita bude wuta na tsawon watanni biyu a Yemen, tare da fatan kara yin shawarwari don samun zaman lafiya mai dorewa.

Shekaru takwas ana aka yi ana yin yaki tsakanin dakarun gwamnati da ke samun goyon bayan kawancen soji karkashin jagorancin Saudiyya  da kuma 'yan tawayen Houthi dake samun goyon bayan Iran. Majalisar Dinkin Duniya, ta ce yakin da ake yi a kasar ta  Yemen ya yi sanadin mutuwar dubban darurruwan mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu, inda kashi biyu bisa uku na al'ummar kasar ke bukatar agajin jin kai. 


 


News Source:   DW (dw.com)