Hukumar kididdiga ta sanar da haka a cikin rahotonta na wannan wata na Mayu mai karewa, inda ta ce Jamus ta fuskanci tashin farashin da ya kai maki 7.9 cikin 100.
Hukumar ta alakanta tsadar rayuwar da ake fuskanta a Jamus din da rikicin Ukraine wanda ya haddasa tsadar farashin makamashin gas da fetur.
Tun da farko hukumomin kasar sun ce suna tunkarar wannan kalubale ta hanyar rage farashin tikitin jirgin kasa na watanni uku da bayar da tallafi ga man fetur a fadin kasar.