Birtaniya ta shiga cikin tsadar rayuwar da ba ta taba fuskanta tun shekarar 1982 ba. Alkaluman na hukumomi sun ce tashin farashin ya fi shafar farashin fetur da kayan abinci. Hakan dai na zama wani babban tashin farashi da a cikin shekaru nan bai taba faruwa da kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki da Birtaniya ke ciki ba.
Yakin da Rasha ke yi a Ukraine tare da radadin corona ne ake zargi da haifar wa Birtaniya da sauran bangarori na duniya tsadar rayuwar.